Shugaban kungiyar, Dr. Anjorin ya ce sun ziyarci hukumar ta Hisbah ne don nuna goyon bayansu gareta, tare da neman hadin kan hukumar don kamawa _foundation_ din wajen taimakawa al’ummah musamman marasa karfi da marayu.
Kwamandan Hisbah ya ba su tabbacin hukumar zata ba su hadin kai a kan dukkanin wasu tsare-tsare da kungiyar su ke da su na taimakawa al’umma ma damar ba su ci karo da addini ba.


