A kwanakin da su ka gabata ne bayan Hukumar Hisbah ta lalata tarin kayan maye a garin Funtua, reshen Hukumar na Karamar Hukumar Kafur ya kama kayan maye da su ka hada da samfari kala-kala na giya mai yawa. Bayan bin ka’idojin da doka ta tanada, hukumar ta lalata wadannan kayan maye ranar Lahadi 28/7/2024.
Babban Kwamandan Hukumar ta Hisbah, Sheikh Dr. Aminu Usman (Abu Ammar) ne ya jagoranci tawagar shugabannin Hisbah zuwa kona kayan mayen. Wadanda su ka halarci wurin lalata kayan sun hada da Mai Girma Hakimin Kafur Dangaladiman Katsina Alhaji Abdulrahman Rabe Abdullahi, wakilin Shugaban Karamar Hukumar Kafur, wakilin DPO, wakilin Shugaban Hukumar DSS na Karamar Hukumar, wakilin DO na Civil Defence, da tarin ‘yan Hisbah maza da mata daga kananan hukumomin yankin.
A jawabin da ya yi, Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Katsina, Sheikh Dr. Aminu Usman (Abu Ammar), ya yi godiya tare da bayyana yadda Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda PhD ya ke ba Hukumar Hisbah cikakken goyon baya. Ya kuma yaba, tare da yin godiya ga shugabannin hukumomin tsaro na Karamar Hukumar ta Kafur a kan yadda su ke baiwa Hukumar Hisbah goyon baya wajen gudanar da ayyukanta. Babban Kwamandan ya ja hankalin ‘yan Hisbah da su kasance masu bin doka da oda, kuma su sani jami’an tsaro abokan aikinsu ne ba kishiyoyi ba. Ya kuma umurce su da yin hakuri da jin tsoron Allah a cikin aikinsu.
Babban Kwamandan ya bayyana yadda cikin ‘yan watanni Hukumar ta Hisbah ta dakile fatauci da shan kayan maye a cikin Jihar Katsina. Ya ce wannan ya kawo raguwar aikata laifuka da kusan kashi saba’in bisa dari (70%) kamar yadda wasu daga cikin shugabannin hukumomin tsaro na jihar su ka sanar da shi. Ya ce a baya an lissafa Jihar katsina a cikin jihohin da a ka fi ta’ammuli da kayan maye, wanda wanna ya bata tarihin Jihar mai kyau na manyan waliyyai da jagorori da a ka samu a tarihinta.
Ya kuma bayyana yadda hukumar ta yi kokari wajen hana kananan ‘ya’ya mata cigaba da karuwanci a cikin jihar. Ya ce Hisbah ta sha kama kananan ‘ya’ya mata a cikin wannan harkar, tare da bin hanyoyin da shari’ah ta tanada domin gyara rayuwarsu.
Babban Kwamandan ya kuma bayyana yadda abu na farko da ya yi bayan nada shi a kan wannan mukami ya kasance hada kan al’ummar musulmin wannan Jiha baki-daya domin yin aikin Hisbah tare, wanda wannan ya sa kowane bangare ya ke da wakilci a cikin Hukumar ta Hisbah. Ya yi kira ga dukkan musulmi na kowace kungiya, darika ko akida da su cigaba da bada goyon baya ga Hukumar Hisbah.
A jawaban da su ka yi, Shugaban Karamar Hukumar Kafur wanda ya samu wakilcin Daraktan Ilimi Alhaji Aminu Jikamshi, da Hakimin Kafur Dangaladiman Katsina Alhaji Abdulrahman Rabe Abdullahi duk sun yabawa Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina a karkashin jagorancin Sheikh Aminu Usman (Abu Ammar) PhD a kan ayyukan gyaran tarbiyyar da ta ke yi.
Bayan kammala jawabai ne, Babban Kwamandan na Hisbah ya jagoranci tawaga da ta hada da Dangaladiman Katsina, wakilin Shugaban Karamar Hukumar Kafur, ‘yan Hisbah, Jami’an tsaro da sauran al’umma, daga Sakatariyar Karamar Hukuma zuwa wajen gari inda a ka kona tare da lalata dukkan kayan mayen da a ka kama.
A hanyarsa ta komawa gida, Babban Kwamandan ya kai ziyarar girmamawa ga Mai Girma Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi Justice Saddik Abdullahi Mahuta OFR. Galadiman ya yabawa Hukumar Hisbah ya kuma bada shawarwari domin cigaban ayyukanta.




