- Dakile sha da fataucin kowace irin giya a cikin jihar Katsina.
- Dakile sha da fataucin miyagun kwayoyi a fadin jihar Katsina.
- Hana karuwanci a cikin jihar Katsina.
- Ganowa da daukar mataki a kan gidajen akwatawa a cikin garin Katsina.
- Hana badala a cikin otel-otel na Jihar Katsina. Wannan ya hada da hana kai yara kanana otel domin lalata tarbiyyarsu, haduwar maza ko mata fiye da biyu a cikin daki daya wanda wannan na habbaka luwadi da madigo.
- Tabbatar da bin doka ga masu sana’ar acaba (haya da babura) da masu sana’ar tuka kurkura (keke NAPEP).
- Hana tarukan da ke gurbata tarbiyyar al’umma, musamman matasa, kamar taron DJ wanda har fada da sare-sare a kan yi a wurin.
- Hana ‘yanmata masu tsayawa gefen titi da yamma ko da dare domin neman abokan lalata (wato ‘yan good evening).
- Tsabtace unguwanni daga gidajen badala da a ke kai mata domin bata tarbiyyar al’umma.
- Hana caca a fadin Jihar Katsina.
- Gyara tarbiyyar ‘ya’ya da yawa da su ka gagari iyayensu, ta hanyar sa-ido, kula da nasihantarwa har zuwa wani lokaci.
- Sulhunta ma’aurata. Hukumar Hisbah ta gyara aure da yawa da ya kusa mutuwa, wani ma ya mutu amma a ka gyara shi. Akwai kuma wadanda ke zama na shashanci amma Hisbah ta shiga cikin al’amarin su ka tuba su ka yi aure a kan tsarin shari’ah.
- Jan hankalin iyaye maza akan nauyin ‘ya’yansu da su ke yin watsi da su sakamakon mutuwar aure.





