Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, wato Katsina State Hisbah Board, ta kona kayan maye na maƙudan kuɗi jiya Asabar 20/7/2024 a garin Funtua. Daruruwan ‘yan Hisbah ne daga kananan hukumomin Jihar Katsina a karkashin jagorancin Babban Kwamandan Hisbah na Jihar, Dr. Aminu Usman (Abu Ammar) su ka taru a garin Funtua domin kona kayan mayen da tabbatar da lalata su baki-daya.
Taron na lalata giya da kayan maye da a ka kama, ya samu halartar shugabannin al’umma, malamai, jami’an tsaro da sauran mutane da dama wadanda su ka hada da Mai Girma Sarkin Maska Hakimin Funtua, Alhaji Idris Sambo, wakilin Shugaban Karamar Hukumar Funtua, board member na Hisbah Board mai wakiltar Funtua Zone, Alhaji Kamal Sa’idu Alti, jami’an tsaro da su ka hada da DPO, Shugaban NDLEA na Karamar Hukumar, Shugaban CWC, da sauran al’umma masu yawa.
Yayin da ya ke jawabi a wurin taron, Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Katsina, Dr.Aminu Usman (Abu Ammar), ya yabawa rundunar Hisbah ta Karamar Hukumar Funtua da wannan gagarumin aiki da su ka yi. Ya kuma yabawa Mai Girma Sarkin Maska, da jami’an tsaro na Karamar Hukumar, a bisa goyon bayan da su ke baiwa Hukumar Hisbah. Ya kuma ce Hukumar Hisbah Hukuma ce kamar kowace hukuma wadda ba ta bukatar wata hukuma ta fada mata yadda zata yi aikinta, sai dai tana neman goyon baya daga sauran hukumomi domin gudanar da aiki cikin nasara. Babban Kwamandan ya nemi goyon bayan malaman addini da jawo hankalinsu cewa Hisbah ba ta wata akida daya ba ce, a’a ta al’ummar Musulmi ce baki-daya. Inda ya buga misalai da yadda bayan nada shi a kan wannan mukami ya fara da ziyartar malamai na kowace akida domin samar da hadin kai da yin aiki da kowa ba tare da nuna wariya ba. Ya kuma yi yabo da jinjina ga Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda CON a kan cikakken goyon baya da ya ke baiwa Hukumar ta Hisbah.
A jawabansu a wurin taron, Mai Girma Sarkin Maska, member na Hisbah Board mai wakiltar Funtua Zone da wakilin Shugaban Karamar Hukumar Funtua duk sun yabawa Hukumar Hisbah a karkashin jagorancin Dr. Aminu Usman (Abu Ammar) bisa namijin kokari da ta ke yi domin gyaran tarbiyya a Jihar Katsina.
Bayan gabatar da jawabai sai Babban Kwamandan ya jagoranci tawagar da ta hada da Mai Girma Sarkin Maska, manyan jami’an Hisbah, jami’an tsaro da sauran al’umma maza da mata zuwa wurin da a ka kona kayan mayen a Unguwar Dahiru da ke garin na Funtua. Kayan mayen da a ka kona bayan samun izini daga kotu, su na da yawan gaske da kuɗinsu ya kai maƙudan Naira.
Daga karshe Babban Kwamandan ya kai ziyarar girmamawa ga iyayen kasa da malamai wadanda su ka hada da Mai Girma Sarkin Maska Hakimin Funtua, Liman Sheikh Malam Sa’id, Malam Murtala Sa’id Alti, Sheikh Abdurrahman Jibrin, da sauransu.
Bayan kammala taron, Babban Kwamandan ya yi afuwa da nasiha ga wasu mata da Hukumar Hisbah ta kama da laifuka a garin na Funtua, inda nan take ya sallame su domin tafiya gidajensu da fatan zasu gyara halayensu. A kan hanyarsa ta dawowa gida kuma, ya biya garin Malumfashi inda ya kaddamar da ofishin Hisbah na Karamar Hukumar.
Rahoto daga Aminu Aliyu Albany, ACG, ICT, Katsina State Hisbah Board







