Dattawan da ke zaune a unguwar sun bayyana jin dadin ne a lokacin da suka kawo ma hukumar Hisbah ziyara a wannan Litinin ɗin.

Kamar yadda suka bayyana, hotel din na lalata masu tarbiyyar yaya, kwaramniya, da sauran matsaloli.

A nashi tsokacinshi, kwamandan hukumar ta Hisbah Dr. Aminu Usman (Abu Ammar) ya bayyana jin dadi dangane da kawo ziyararsu, inda ya ce zuwan ya ƙara masu ƙwarin gwiwa.

Dr. Aminu Usman ya ja hankalinsu da su ƙara sanya ido akan abubuwan da ke faruwa kusa da su.

A baya dai dattawan unguwar sun ce sun yi ƙoƙarin ganin sun shawo kan abinda ke faruwa unguwar, amma abun ya gagare su sai zuwan wannan hukumar.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *